Rashin ɗa’a da cutarwa

Ta la’akari da manufarmu da kuma ɗabi’unmu, CLEAR Global ta himmatu wajen kiyaye manyan matakan ɗa’a a tsakanin dukkanin ma’aikatanta, haka kuma ta na tsammanin tarbiyya gami da ɗa’a daga dukkanin ma’aikatanta tare da nuna kyawawan halaye, nagarta, jajircewa, da haƙuri yayin aiwatar da ayyukansu. Dukkan ma’aikata, masu neman ƙwarewa, ma’aikatan sa kai, haɗi da masu bayar da shawara, na aikine ƙarkashin Doka da Oda. Haka kuma dukkanin ƙungiyoyi abokan hulɗa, ana tsammanin su da bayar da haɗin kai na tabbatar da sun kiyaye kyawawan ɗabi’un da aka zayyana a wannan jadawalin tare da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa.

CLEAR Global na ɗaukar bin doka da muhimmanci. Idan ku na da ƙorafi game da halayyar wani daga cikin ma’aikatan CLEAR Global, za ku iya kai rahoto:

Yayin bayar da rahoto, akwai buƙatar bayar da gamsassun bayanan da za su taimaka, kamar kwanan wata, lokacin da abin ya faru, yanayin ƙorafin, da wanda ke da hannu a ciki, shaidu, yadda lamarin ya faru, idan akwai barazana ga lafiyar wani, musamman yara ƙanana, sannan kuma idan akwai wani sashen da su ma aka kaiwa wannan ƙorafin.