CLEAR Global logo

Tattaunawa Biliyan 4

Kawo sauyi a intanet ta fuskar sadarwa. Ya ba mu damar samun bayanai mara iyaka, kuma ya ba mu damar yin hulɗa da juna kamar ba a taɓa gani ba, duk inda mu ke. Duk da haka, albarkatun harshe, kamar fassarar inji, fahimtar magana ta atomatik, da manhajar AI na tattaunawa, da kuma babbar fa’idar da su ke kawowa (saƙonnin nan take, sadarwa ta hanyoyi biyu, buɗe bayanai), na samuwa ne kawai ga rabin al’ummar duniya. Mutane biliyan hudu ba za su iya samun bayanai a intanet cikin yarensu ba.
A hand of an African person holding a mobile phone

Fiye da mutane biliyan 4 a duniya ba za su iya samun bayanai ko sadarwa ta hanyar fasahar zamani ba, saboda kaɗan ne ko ku babu wani abu a cikin yarukan da suke magana da su.

Lokaci ya yi da za a yi aiki

Idan aka ce akwai ƙarancin hazaka a fasahar yare a faɗin Afirka kudu da hamadar Sahara, Kudancin Asiya da sauransu, waɗannan al’uma za su fuskanci ƙarancin yadda fasahar su za ta haɓaka. Sannan aikace-aikacen fasaha na haɗe yarukan da aka ware na ci gaba a hankali. Tazara digital language na ƙara faɗaɗa.

Lokaci ya yi da za mu yi aiki, kuma ba za mu iya yin wannan mu kaɗai ba. Mu na buƙatar taimakon ku. Mu na da damar yin amfani da fasaha don haɓaka ci gaba, samar da ƙarin daidaito, da ba wa mutane dama kan rayuwarsu.

CLEAR Global ta haɗa gwanaye ta amfani da harshe a ma’aunin manhajar AI ​​bisa ƙwarewar tallafin ayyukan jin ƙai na ƙasa da ƙasa don magance rarrabuwar language dijital. Wannan haɗin gwanaye na musamman zai ba mu damar yin aiki a matsayin ma su da sauyi, gina hanyoyin magance matsalar yare na manhajar AI tare da babban tasirin zamantakewa.

Za ku iya taimakawa.

Mu na neman goyon bayan ku. Mu na neman abokan hulɗar tasirin zamantakewa, masana fasaha na gida, shirye-shiryen asali, ma su tallafawa, ma su bayar da gudummawa, da sauransu don taimakawa wajen kawo mutane biliyan 4 cikin tattaunawar duniya, amma a fara da nasu, na gida. Za ku iya aiki tare da mu?

Isa ga ƙarin mutane

Ba da gudummawa don tallafawa wasu biliyan 4

Ƙara koyo

Yaɗa bayani

Yaɗa bayani game da tafiyar Tattaunawar Biliyan 4.

Sauke kuma ka aika

Karanta shafukan mu ɗaya bayan ɗaya

Bukatar tana da ban mamaki, da gaggawa: canjin yanayi , hijira, tallafawa mata da ƴan mata da ayyukan samun kuɗi da samun damar bayanan haifuwa lafiya, da kuma mahimman ayyukan kiwon lafiya da a aynzu COVID-19 – – babu ɗaya daga cikin waɗannan da za a jira.

 

Tuntuɓe mu don haɗin gwiwa ko ɗaukar nauyin tafiyar.