Ku na goyon bayan mutanen da yaƙin Ukraine ya shafa?

Waɗannan kayayyakin na ku ne.

Bayananmu da abubuwan da ake buƙata a aikace na iya taimaka mu ku wajen fuskantar ƙalubalen yare da sadarwa

– Aукраїнська, polski, Română, русский, Magyar, slovenčina, čeština, Deutsch.

 

Me ku ke son yi?

Latsa nan don tsallakawa zuwa sashen.

People traveling through Krakow station

Yi sadarwa iya yawan yadda za’a fahimta 

Duk yaren da ka ke amfani da shi, nemi yadda za ka yi amfani da sassauƙan harshe don tabbatar da mafi yawan masu saurare sun fahimce ka. Mene ne sassauƙan harshe? Sauke takardar shawarwari cikin Ingilishi українська polski Română русский

Yi sadarwa yadda ya kamata tsakanin harsuna 

Yadda za a sami, aiki tare da, ko aiki a matsayin mai tafinta ko mai fassara a aikin jin ƙai na gaggawa.

Zanen alamomin magana - aikin jin ƙai na Ukraine na tattaunawa tare da masu aikin jin ƙai da masu agaji

Shawarwari a aikace ga masu fassara na al’umma

Shirya sosai don yin tafinta da kuma sadarwa yadda ya kamata.

Ingilishi українська polski Română русский

Zanen mace tare da allon zane

Jagorar yin tafintan aikin jin ƙai da shiga tsakani na al’ada don masu aikin jin ƙai da masana harshe

shawarwari ga masu aikin jin ƙai da ke aiki da masu tafinta kan batutuwa masu muhimmanci

Shawarwari shida ga masu aikin jin ƙai da ke aiki da masu tafinta kan batutuwa masu muhimmanci da CLEAR Global da Oxfam su ka Samar

Ingilishii українська polski Română русский Magyar slovenčina  Deutsch

Yadda za a yi aiki tare da masu tafinta da masu fassara – jagora ga ƙungiyoyi, masu aikin sa kai da sauran masu agaji

Ingilishi New call-to-action New call-to-action   New call-to-action   New call-to-action

Duba wannanƙunshin bayanan masu tafintadon tallafawa yaren da ke kusa da ku.

Sanar da muhimman batutuwan jin ƙai

A san irin kalmomin da za a yi amfani da su wurin sanar da kariya, ɗaukar nauyi da kare cin zarafi ta hanyar jima’i, keta haddi da matsantawa (PSEA) a aikin agaji a Ukraine. Samu damar maganganun masana da kayayyakin horarwa na harsunan da suka dace.

Cibiyar Taimako ta Ukranie (Ukraine Aid Center) da aka rubuta da shudin launi akan yalon alama cikin yaren Polish da Ukrainian - kibiya na nuna dama

Jerin ma’ana a harsuna da yawa na PSEA – cikin Ingilishi– українська – polski –Română – русский – Magyar – slovenčina, čeština – Deutsch

mace da yaro ɗauke da buhhunansu da jakunkuna tare da su, ma’aikacin agaji da sauran mutane a gaba

Jerin ma’anonin kariya da ɗaukar nauyi na Oxfam – a Ingilishi – українська – polski – Română – русский

jajaye da korayen barguna a ninke an tara su a tashar jirgin ƙasa a Krakow agajin Ukraine

Ainihin ƙai’idoji da suka danganci cin zarafi da amfani da dama ta hanyar jima’i a harshe-mai sauƙi – a Ingilishi – українська – polski – Română, русский – Magyar – Deutsch

Ba Uzuri ga Cin Zarafi gabatarwar bidiyon PSEA ga sababbin masu aikin agaji da ƴan kwangila – A Ingilishi – українська – polski – Română – русский– Magyar – slovenčina – čeština – Deutsch

A san irin harshen da za a yi amfani da shi yayin

Gano waɗanne bayanai ake da su kan yarukan da mutane ke magana don taimaka muku tsara ayyuka cikin yarukan ga masu amfani da su a kuma tabbatar masu magana da tsurarun yaruka sun sami bayanan da su ke buƙata.

Dandalin Bayanan Amfani da Harshe kan Agaji a Ukraine

 Dandalin musayar bayanai da ya hadar da kafofi masu yawa don bawa masu aikin agaji cikakkar dama da kuma sabuwar mahanga ta harsuna da kuma hanyoyin sadarwa da jama’ar da yaƙin Ukraine ya shafa ke amfani da su.

Taswirar yaren da ake hulɗa da shi don Ukraine

Bayanin da za a iya kalla wanda ke nuna wuraren da mutane ke magana da yaruka sama da ashirin da aka ɗauka a faɗin Ukraine. 

Masu aikin agaji za su iya amfani da shi don fahimta sosai da tallafawa jama’ar da rikici ya shafa.

Harshen Romani takardar bayanin gaskiya Fahimci yadda jama’a ke amfani da harshen Romani a tsarin agaji a Ukraine ta New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action
Tool icon

Yi amfani da kayan aikinmu ku tattaro bayananku game da buƙatun harshe da hulɗoɗiin mutanen da su ke amfani da ayyukan da ku ke yi. 

An tanadi tambayoyi ga ɗaiɗaikun mutane, iyalai da jin ra’ayin muhimman masu ba da bayanai da aka tsara na Kobo Toolbox/ODK. An tanada a harshen čeština, Magyar, Română, русский, slovenčina, українська, Deutsch, polski, da Ingilishi a shafin yanar gizon TWB.

Miliyoyin jama’a sun yi hijira daga Ukraine. Sama da wasu Miliyoyin na neman mafaka a ƙasashen waje. Taimaka don tabbatar da sun samu muhimman bayanai cikin yarensu.

Yaɗa bayanai tare da jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine

Kompas wani dandalin harsuna ne masu yawa na na’ura mai fikirar dan Adam da ke ajiye bayanan da aka tantance, yanzu-yanzu don jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine a harsunan Ukrainian, Polish, Romanian da Russian. Wannan na taimakawa mutane samun amsoshin da su ka shafe su don su fahimci haƙƙoƙinsu, su sami taimako, kuma su yanke hukunci kan me za su yi nan gaba. Don tallafawa jama’a samun bayanai cikin sauƙi sosai a yaren da su ka fahimta, ƙungiyoyin bayar da agaji za su iya:

  • Yaɗa bayananku ga jama’ar da yaƙin ya shafa ta hanyar Kompas
  • Saka Kompas a shafin yanar gizonku don tallafawa mai amfani da ita sosai
  • Tattauna ta yin amfani da Kompas a matsayin kayan aikin tawagar shirinku da masu ɗaukar layin waya

Don ƙara koyo, tuntuɓe mu.

Fahimci ƙalubalen sadarwa da jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine ke fuskanta a kasarku

Duba taswirar labaranmu don ganin muhimmancin yare ga mutanen da yaƙin Ukraine ya shafa, da dalilin hakan ga ingantaccen aikin agaji a Ukraine da ƙasashe maƙwabta

Karanta shaidar shigar da yaree cikin aiki agaji 

Sadarwa ƙalubale ne cikin aikin agaji, ko da a wuraren masu amfani da ayyuka da masu samar da ayyukan ke magana da yare guda.

Mu na magana da mutanen da yaƙin ya shafa kai tsaye, ƙungiyoyin agaji, da masana harshe a ƙasashe uku da ke ɗaukar nauyin mafi yawan jama’ar da aka tilastawa tserewa daga Ukraine. Karanta hangenmu da shawarwarinmu na yadda ma’aikatan agaji za su magance tarnaƙi na harsuna kuma su harhaɗa tallafi ga yare don samun nasara kan manyan ƙalubale.

  • Sanin harshe da giɓi a harshe a agajin Ukraine – taƙaitaccen rahoto cikin Ingilishi – New call-to-action   New call-to-action
  • Hasashe da Fassarar Google – Rahoton ƙasar Romania cikin New call-to-action New call-to-action   New call-to-action
  • Kwantan bayanai, sabon taƙaice – rahoton ƙasar Moldova cikin New call-to-action New call-to-action New call-to-action New call-to-action
  • Dudduba gibin bayanai a harsuna huɗu – rahoton ƙasar Poland cikin New call-to-action New call-to-action   New call-to-action

Amfani da yare da kuma asalin harshe na iya zama na takatsantsan, ana buƙatar ma’aikatan agaji su fahimci wadanne yaruka jama’a ke buƙata ko su ka zaɓi su yi hulda da su. 

Karanta rahotonmu kan yadda amfani da yare da asalin harshe ke canzawa a Ukraine don fahimtarwaɗannan muhimman abubuwan sosai da tsara dabarun sadarwa da su ka dace kuma masu tasiri.

Sake zana taswirar harshe na Ukraine – rahoto cikin –  New call-to-action New call-to-action New call-to-action

Kasance cikin samun sabon bayani 

Shiga jerin waɗanda za mu aikawa saƙoza mu tura maka bayanan sabbin ayyukanmu.

Taimaka ya isa ga jama’a da yawa 

Samu gudunmawar harshe

 Ma’aikatan agaji – ƙara tasirinku ya isa ga jama’a da yawa tare da muhimman kayayyaki da ayyuka cikin harshen da ya dace.

Ba da gudunmwa don tallafawa aikinmu

Gudunmawarku na taimaka mana wajen samar da ayyukan harshe da wuri don mu gina sabbin mafita ga jama’ar da yaƙi ya shafa.

Bayar da gudunmawar fassara

Yi aikin sa kai tare da mu.
Bayyana gwanintarka ta harshe ga aikin ƙwarai. Shiga TWB don taimakawa aikin gaji.