Ayyuka

Zamo wani ɓangare na kawo sauyi. Sanya aikinku ya zama mai muhimmanci. Zamo wani ɓangare na CLEAR Global.

CLEAR Global na taimakwa mutane samun mahimman bayanai kuma a ji su da kowane yare su ke magana. Ƙungiyarmu ta ƙasa da ƙasa ta ƙware don cimma wannan manufa.

Saurari Aimee Ansari, Babbar Jami’ar Gudanarwa, ta CLEAR Global

Our Nigeria team

Yin aiki tare da mu

Al’adun mu

CLEAR Global na haɓaka al’ada bisa bayyananniyar sadarwa, girmamawa, da amana. Idan kun kasance tare da mu, za ku zama wani ɓangare na ƙungiyar mutane daban-daban daga ko’ina cikin duniya.

Tare da mu, za ku yi aiki cikin fikira da ƙirƙira a cikin rukunai. Tunaninku da ra’ayoyinku ko yaushe za su kasance masu ƙima, da yin la’akari da su, kuma galibi ana shigar da su.

Banbancinmu shine, Daidaito, da Shigarwa na aiki tare da jagorancinmu don mai da CLEAR Global ƙungiyar da ake mutunta kowa cikin mutunci. Ba za a taɓa amincewa da kowace irin wariya ko tsangwama ba a CLEAR Global. Mu na ɗaukar aikinmu da muhimmanci, kuma mu na yi wa juna uzuri. Abin da mu ke yi zai iya yin tasiri mai muhimmanci ga rayuwar wasu. Mu na son sanya ƙwarewarku ta zamo mai sakamako.

Ayyukan da mu ke da su a yanzu

Idan ku na son shiga ƙungiyarmu don sauya yanayin sadarwar duniya, duba guraben ayyukanmu kuma a nema a wannan wuri mai zuwa:

Darajarmu

Al’adunmu sun samo asali ne zuwa mahimman ɗabi’u shida da mu ke haɓakawa a matsayin ƙungiyar sa-kai tare da dalili mai ma’ana:

Mafi kyawu

A matsayinmu na jagorar sadar da bayanan jin ƙai a cikin yaren da ya dace, CLEAR Global jagora ce a cikin masana’antar fassara da kuma ɓangaren ƙungiyoyin da ke aiki ba don riba ba.

Mutuntaka

CLEAR Global ta yi imanin cewa kowane mutum, ko mutanen da mu ke yi wa aiki, masu aikin sa kai ko ma’aikatanmu, na da ƙima, sun cancanci girmamawa, da kuma daraja ta asali.

Ƙarfafawa

CLEAR Global ta yi imanin yin amfani da yare don ƙarfafa mutane a duniya don sarrafa ci gaban kansu da makomarsu.

Sabon tsari

CLEAR Global ta fahimta kuma ta na farin ciki da ƙarfin ƙirƙira don magance matsalolin jin ƙai da rikice-rikice a duniya.

Ɗorewa

CLEAR Global ta fahimci cewa cimma manufar mu na buƙatar kafawa da kiyaye ingantattun kayan aikin kuɗi da ƙungiyoyi.

Juriya

Ma’aikatanmu da masu aikin sa kai ma su matuƙar ilimi ne da ƙwarewa; su na martaba juna, abokan hulɗarmu da waɗanda mu ke wa aiki; samar da yanayin aiki mai daɗi; kuma su na gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa a kowane lokaci.

Ya kamata mazauna Amurka da ma su neman zama ƴan Amurka su lura da cewa mu na shiga E-Verify, kuma mu na mutunta ƴancin kowa na yin aiki. Ba ma nuna wariya dangane da zama ɗan ƙasa, matsayin shige da fice ko wani abu daban. Idan an ba ku izinin yin aiki bisa doka, ku na da ƙwarewa da gogewa, mu na so mu ji daga gare ku!

Yanayin aikin mu

CLEAR Global na aiki da ma’aikata ma su aiki daga gida a ko ina – wannan yana ba mu sassaucin da mu ke buƙata don aiki da haɓaka ma’aikatanmu. Hakan na taimaka mana rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa, don haka za mu iya saka ƙarin kuɗi don taimaka wa mutane. A ƙarshe, amma ba a ƙalla ba, haka na taimaka mana rage tasiri ga muhalli.

Yayin da mu ke aiki a cikin yanayi mai sauri, mu na bunƙasa wurin aiki cikin gaskiya don ƙarfafa ƙirƙira, yawan aiki, da haɗin kai. Mu na aiki tuƙuru don kiyaye abokantaka da kulawa. Tawagarku za ta yi bakin ƙoƙarinta don tabbatar da kun fahimci aikinmu da matsayinku daga ranar farko.

Mu na dogara ga kayan aikin intanet don sadarwa da haɗuwa. Mu kan yi taro duk wata na dukkanin maʻaikata, inda mu ke musayar labarai da sabuntawa, cikin raha, da ƙara sanin juna sosai. Har ila yau, mu na tsara shirye-shiryen gabatarwa, taron bita, da sauran tarukan da ke taimaka mana koyo da aiki mafi kyau.

Amfaninmu

Mu na ƙoƙarin sanya ma’aikatanmu jin ƙima kuma a san su. Bugu da ƙari mu kan sanya gasa, kuma mu na bayar da:

  • awannin aiki da su ka dace da wuri,
  • kwanaki 20 na hutun shekara da kwanaki 10 na hutun gama gari,
  • abubuwan jin daɗi da tallafin da ya dace,
  • damar koyo, da sauransu.

Ma’íkatanmu

Tsarin ɗaukar ma’aikata

Neman aiki na ɗaukar lokaci da ƙoƙari. Mu na ƙoƙari mu kasance ma su gaskiya yadda za mu iya a cikin tsarin ɗaukar ma’aikata.

  • Mu na wallafa jerin albashi don nuna mataki nauyi da matsayin mutum. Lokacin da aka zaɓi wanda ya dace kuma ya yi nasara mu na gano ainihin adadin shekarun ƙwarewarsa na aiki. Yayin da a wasu wuraren ake ba da adadin wani kuɗi na fara aiki, to mu ba haka tsarinmu ya ke a CLEAR Global ba. Mu na amfani da wannan don tabbatar da daidaito tsakanin ɗaiɗaikun mutane na al’adu daban-daban tare da tabbatar da cewa babu son rai ko hasashe da ke tasiri ga shawararmu. Mun gane hakan na iya bambam ta mu da sauran ƙungiyoyi. Mu na tsammanin haka ya fi dacewa kuma a bayyane don gaya muku abin da za ku iya tsammanin samu.
  • Wasiƙar gabatarwa zaɓi ce. Mun san cewa wasu ma su neman aiki na son rubutawa wasu kuma ba sa so. Zaɓi ya rage na ku.

Danna don ƙarin koyo game da kowane mataki na tsarin.

Mataki 1: Neman aiki

Gano yadda ake rubuta wasiƙar neman aiki yadda ya dace.
Gina CV ɗinka ta hanyar bayyana ƙwarewarka.
Rubuta wasiƙar gabatarwa idan ka na son ƙara bayani
Amsa dukkanin tambayoyin neman aikin.
Duba saƙon imel ɗinka akai-akai!

Mataki na 2: Bibiya

Koyi yadda mu ke bibiyar takardun neman aiki.
Tawagarmu ta HR na duba duk takardun neman aiki
Mu na zaɓar sunayen waɗanda su ka dace tare da tuntuɓar waɗanda aka zaɓa zuwa mataki na gaba.

Mataki na 3: Auna Fahimta

Ga bayanin matakan da ake bi don auna fahimta.
Gwaje-gwaje sau da dama ta bidiyo ko a rubuce, ana yin su bisa tsarin ku.
Masu neman aiki da ke da buƙata ta musamman na iya neman tallafi.
Za mu sanar da sakamako ga duk wanda aka yi wa gwaji.

Mataki na 4: Tattaunawa

Fahimci abin da ya faru yayin tattaunawa!
Mu na gudanar da tambayoyi ta bidiyo na mintuna 45/60 tare da membobin kwamiti 3.
Mu na son jin amsoshinku da tambayoyinku cikin gaskiya.
Za mu iya ba ku aikin, da kuma sanya ku a cikin jerin jadawalinmu ko yanke shawara ba za ku ci gaba ba.

Mataki na 5: Takardar ɗaukar aiki

Wannan shine mataki na ƙarshe kafin fara aiki!
Wanda ya yi nasara za a bayyana masa matsayinsa bayan mun kammala bincike guda uku.

Mataki na 6: Fara aiki

Makonninka na farko za ka kasance tare da mu.
Za a yi maraba da ku a manhajar Slack.
Za ku yi koyo game da manufofinmu, matakai, da al'adunmu.
Za ku sami kiran tattaunawa tare da membobin ƙungiyar - da sauransu!