Game da tattaunawar biliyan huɗu

lafiyar alʻuma

A CLEAR Global, mu na taimakawa jama’a su sami ingantattun bayanan kiwon lafiya, da kowane yare su ke magana.

Matsalar ita ce: rashin fahimta da rashin bayani na barazana ga lafiyar al’uma

  • Rashin bayanan da su ka kamata da rashin fahimta na kara tsananta barkewar cututtuka, ya na sawa su zama da wahala a magance su da kuma killace su.
  • Rashin amincewa da abinda ya janyo su da jita-jita ke haifarwa na hana mutane da yawa samun kulawar ƙwararru. Irin wannan lamarin ya kasance game da jinkirin rigakafin COVID-19 a ƙasashen Afirka 15Amurka, Turai, da ɓarkewar cutar Ebola a Arewacin Afirka .
  • Shingayen harshe na iya zama babban dalilin rashin samun bayanai. Fahimtar bayanin lafiya na raguwa da kaso 78% idan ba a bayar da shi a cikin yaren ɗan adam ba.

"Sun taimaka mana da gaske wajen fahimtar ƙalubalen da jama'a ke fuskanta, gami da cikakkun bayanai game da yanayin rayuwarsu, da haɗarin lafiya. Haka kuma, ya na taimaka mana mu daidaita ayyukanmu da al'adun al'umma, kuma hakan ya haɗa da isar da saƙon cikin harshensu na gida.

Sanni Bundgaard
IRC

Mafitar CLEAR Global

CLEAR Global na ba da bayanan ceton rai yayin rikice-rikicen lafiya don taimakawa ingantacciyar hanyar tunkarar ɓarkewar cututtuka da isar da ingantattun bayanai.

Mu na yin bincike don fahimtar bayanan jama’a da buƙatun su na sadarwa. Sannan mu na haɓaka hanyoyin sadarwa waɗanda ke ba jama’a damar shiga su bayar da bayanai cikin yarensu. Kuma mu na yin haɗin gwiwa tare da ingantattu, amintattun masu bayar da amsa don faɗar bayanan lafiya a cikin nau’ikan harsuna da yawa da aka yi gwajinsu.

A Kenya, mun gano giɓin sadarwa da ke shafar samun bayanan cutar Ebola. Mutum 1 cikin 5 ne kaɗai ke fahimtar Ingilishi sosai – mutane na buƙatar bayanai cikin Swahili. Wannan ya taimaka wajen ba da fifiko ga fassara zuwa Swahili don tabbatar da samun ingantacciyar hanyar samun bayanai da kuma yaƙi da rashin fahimta a duk faɗin ƙasar.

A Najeriya, mun samar da Manhajar Shehu, manhajar chatbot don tattaunawa a harsuna da yawa da aka tsara don isar da ingantattun bayanan COVID-19 da cutar Ebola a Hausa, Kanuri, da Turanci. A watanni shida da ƙaddamar da shi, Shehu ya yi musayar saƙonni sama da 80,000 tare da masu amfani da fiye da 5,750, inda ya samu amincewar kashi 90.1%.

A Bangladesh, mun haɓaka ƙa’idodin yaren Rohingya, ta yanda ma’aikatan kiwon lafiya za su iya sadarwa tare da mutane. Abubuwan da mu ke amfani da su na taimakawa wajen yaɗa ingantattun bayanai da kuma samun amincewar mutane a cikin tsarin, don haka suna jin daɗin neman tallafin kiwon lafiya da na magani.

CLEAR Global na buƙatar taimakonku don

shiryawa da kuma mayar da martani ga ƙalubalen kiwon lafiyar duniya.