Sabin albarkatu

Sanya jama’a a tsakiyar fasahar jin kai.

Littafin koyo mai amfani don tsarawa da amfani da fasahar zamani a cikin lokacin gudanar da aikin jin kai ta hanyar hanyoyin da al’umma ke jagoranta, waɗanda suka mayar da hankali kan ɗan adam.

CLEAR Global na taimakawa jama'a samun mahimman labari kuma a ji su, da kowane harshe da su ke magana da shi.

Muna cimma wannan manufa ta hanyar sabbin bincike da shirye-shirye na duniya, fasahar harshe, cibiyoyin harshe, ƙwararrun ma’aikata, da kuma al’umma sama da dubu ɗari biyu a cikin ƙasashe ɗari da arba’in da takwas na masana harshe.

Kaso ashirin da takwas cikin ɗari

Kaso ashirin da takwas cikin ɗari na ƴan gudun hijirar Rohinja da aka yi nazari a dubu biyu da sha takwas waɗanda su ka ce ba su da isasshen labari don yanke shawara.

Biliyan huɗu

Akwai kusan jama’a biliyan huɗu da ke magana da harshen da aka ware, wanda ake barin su a baya wurin tattaunawa mai muhimmanci a duniya.

Sama da tamanin

Mun tallafawa shirye-shirye da abokin hulɗa cikin ƙasashe sama da tamanin, a harshe sama da ɗari biyu da ashirin.

Sababbin hanyoyin ƙarfafa gwiwar jama’a ta hanyar harshe da fasaha

Translators without Borders

Ƙarfin ikon ma’aikatan sa kai masana harsuna sama da dubu ɗari biyu da ke sadaukar da kai don cike giɓin harshen duniya da kuma ba da martani wurin amsa buƙatunsu cikin sauƙi.

Fasahar harshe

Harsuna sha bakwai ne kawai suka mamaye abubuwan da ke cikin dijital, kuma waɗannan ba su ne harsunan farko na al'ummomin da rikicin ya shafa ba. Muna da shekaru da yawa na gogewa wajen gina fasahar harshe ga harsunan da ba su da albarkatun fasaha.

Bincike da bayanan ƙididdiga

Binciken mu ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa waɗanda galibi ba a magance su sosai ba, suna mai da hankali kan batutuwan da suka cancanci a yaba musu da kuma fahimta sosai.

Ayyukan harshe da sadarwa

Muna bayar da ayyukan harshe a cikin harsuna sama da ɗari biyu. Muna alfahari da samar da ingantattun hanyoyin magance harshe, waɗanda ke samun goyon bayan al'umma mai yawa ta masana harsuna.

Ziyarci shafin yanar gizo na Translators without Borders.

Rohingya Interpreter (center) works with a doctor (back right) to explain medication dosage instructions at a new medical facility in Kutupalong makeshift camp near Cox's Bazar, Bangladesh. Photo_ Eric Deluca _ TWB

Mafi girman ma’aikata masana harsunan jin ƙai a duniya, Translators without Borders

Al’ummarmu ta duniya mai masana harsuna da masu fassara sama da dubu ɗari biyu suna da muhimmanci a cikin manufarmu. Sha’awarsu da ƙwarewarsu na rufe gibin harshe a duk duniya.

Dandalin TWB

Dandalin mu na haɗa ƙungiyoyin agaji da ƙwararru a fannin harshe don samar da bayanin ayyukan lafiya, jin ƙai, da na haƙƙin ɗan adam a harsunan gida.

Ayyukan harshe

Ayyukanmu na harshe suna taimaka wa ƙungiyoyin sa-kai na duniya da na gida su yi mu'amala da jama'a da ke cikin mawuyacin hali yadda ya kamata. Muna taimakawa wajen isar da muhimman labari cikin sauri, cikin harshen da ya dace.

Fasaha da magance matsalar bayanai

Ta hanyar horar da masu fassara, da ƙirƙirar ƙamus na harsuna da yawa, da haɗin gwiwar bincike da fasaha, mu na ƙarfafa bunƙasar harshe.

"Ban taɓa tsammanin za a iya ɗaukar harshe na da muhimmanci sosai har a saka a na'ura ba.”

Za ku iya taimakawa wajen cike gibin da ke tsakanin harshe.

Wannan tsarin yana aiki kuma buƙatar taimako da gaggawa. Kowace rana, ana barin jama’a da yawa a baya saboda harshen da suke magana. An tabbatar da hanyoyin mu.

Yanzu, muna buƙatar taimakon ku don faɗaɗa shi.

Mun zarce yadda ake tsammani.

Ana kiran CLEAR Global da suna Translators without Borders a da. Mun girma cikin sauri a cikin shekaru biyar da suka gabata, kuma wannan sunan ba ya nuna duk abin da muke yi – amma har yanzu yana nan a matsayin babban sashinmu kuma tushen aikinmu.

Ziyarci shafin yanar gizon Translators without Borders.