Al’umar da ke magana da yaren da aka ware na buƙatar taimakonku cikin gaggawa.
Mutane biliyan huɗu ne ke ware a halin yanzu daga tattaunawa mai muhimmanci. Taimaka don samar da muhallin da kowa zai sami bayanin da ya dace kuma a saurare shi, da duk irin yaren da su ke magana da shi.
Biliyoyin mutane ne ke tattaunawa ta fasahar zamani kowace rana. Mun dogara ga intanet don amsa tambayoyi masu muhimmanci kuma mu shiga cikin tattaunawar gaggawa a yarukan da a ka fi amfani da su a intanet kamar Ingilishi, Sinanci, da Sipaniyanci.
Amma har yanzu, sama da mutane biliyan huɗu ba sa iya samun dama ga ainihin haƙƙinsu na samun ingantattun bayanan da za su dogara da su – saboda ƙaranci ko babu a yarensu. Gudunmawarku na taimaka mana haɓaka muhimmancin yare da kayan aiki don taimakawa mutanen da su ka yi hijira daga gidajensu, waɗanda ke fuskantar matsala ko bala’i, samun bayanan ceton rai kuma a saurare su.
Bisa taimakon Translators without Borders, CLEAR Global na haɓaka tattaunawar duniya, da sauraron al’uma, ko da a wane yare su ke magana.
Ƙungiyar CLEAR Global na amfani ƙwarewar shekaru a ayyukan jin ƙai na ƙasa-da-ƙasa don ba da fifikon yare da fassara kan abinda ya shafi rikice-rikice ta ayyukan jin ƙai duniya. Mu na amfani da ƙarfin fasahar yare, kuma mu na samar da mafita don taimakawa cike giɓin yare a zamanance. Mu na haɓaka manhajar yaruka ta chatbot, da shigifar bayanai don sauraren sauti, taswirar yaruka, da sauran kayan aikin tushen bayanai don tafiyar da canjin yanayi a cikin sadarwa, da sanya buƙatun mutane a gaba.
A shekarar 2022 kaɗai:
- Mun haɗa kai da ƙungiyoyi sama da 45 don taimaka wa mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita a Ukraine don samun muhimman bayanai da yarurrukansu,
- Mun sake buɗe manhajar chatbot da mu ka yi wa laƙabi da Shehu, da ke baiwa al’umar arewa-maso-gabashin Najeriya damar samun amsoshin tambayoyinsu game da COVID-19 a yaren Hausa da Kanuri
- Sannan mun tsara kundin bayanai ma su amfani da AI don taimakawa al’umar Bihar da ke India game da yadda za su koyi noma ta hanya mai sauƙi.
Tallafa, don bunƙasa tsarin tafiyarmu ta Four Billion Conversations movement
Kasance mai ba da shawara don sauraren mafi yawan muryoyin da aka ware. Mu na son shigar da mutane biliyan hudu cikin muhimmiyar tattaunawar duniya wadda ta shafe su.
Ba da gudummawa ga CLEAR Global a yau (USD).
Tallafinku ku na da muhimmanci. Taimaka wajen ƙirƙirar hanyoyin sadarwar da ke aiki ga kowa, ko da wane irin yare su ke magana.
Ƙara koyo kuma yaɗa kalmar: #4BillionConversations #4BC