Martanin ƴan gudun hijira

Tallafawa al’umar da aka tilastawa gudun hijira

Kowane mutum na da haƙƙin samun muhimman bayanai kuma a saurare shi, ko wane yare yake magana.

Rohingya refugee camp in Bangladesh

Adadin mutanen da aka tilastawa yin gudun hijira a faɗin duniya ya kai miliyan 100.

Fiye da kashi biyu bisa uku na ƴan gudun hijirar sun fito ne daga ƙasashe biyar kawai: Syria, Venezuela, Afghanistan, Sudan ta Kudu, da Myanmar.

Rikicin Ukraine ya tilastawa mutane fiye da miliyan shida yin hijira.

Mutanen da su ka rasa matsugunansu na buƙatar taimako daga duk inda suka fito – don dacewa da sabuwar rayuwa, samun gidaje, aiki, ilimi.

Amma, duk su na fuskantar matsalolin yare da sadarwa.

CLEAR Global na aiki don shawo kan waɗannan shingen. Mu na taimaka wa ƴan gudun hijira su sami mahimman bayanan da suke buƙata don zama cikin aminci a ƙasar da su ka je. Mu na ba da mafitar harshe da ke taimakawa mutane samun amsoshin tambayoyinsu a cikin yaren da su ke fahimta. Ƙwarewarmu na taimakawa wajen cike giɓin sadarwa tsakanin ƴan gudun hijira da al’umar da su ka karɓi bakuncin – da duk yaren da su ke magana .

Rohingya woman during a focus group session

Ƙara koyo game da yadda mu ka tallafawa martanin ƴan gudun hijira a Turai, Kudancin Asiya, da Latin Amurka.

Amsar ƴan gudun hijirarmu na Ukraine

Fiye da mutane miliyan 6 sun tsere daga Ukraine, zuwa Poland, Hungary, Slovakia, Romania, Moldova, da sauran ƙasashe. Nan da nan mu ka samar da wani rukuni don bayar da tallafin yare kyauta ga ƙasashe masu masaukin baƙi da ƙungiyoyi masu tallafawa. Mun kuma aika ma’aikatan mu na duniya zuwa ƙasashe biyar masu masaukin baƙi don tantance buƙatun yare da sadarwa da hanyoyi. Mun ƙirƙiri albarkatun yaruka da yawa da kayan horo don ayyukan jin ƙai da manufar ayyukan jin ƙai. Ya zuwa yanzu, mun fassara sama da kalmomi miliyan 1.3 a matsayin wani ɓangare na ayyuka 178 da aka kammala tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi 31. Ƙara koyo game da martanin ƴan gudun hijirar CLEAR Global na Ukrain.

 

Ukrainian refugees in Poland
Rohingya child refugees in Bangladesh

Martanin ƴan gudun hijirar Rohingya

Fiye da ƴan Rohingya 600,000 ne suka tsere daga Myanmar zuwa Bangladesh a cikin 2017. Yaren Rohingya na ɗaya daga cikin yaren da aka fi nunawa wariya a duniya. Sakamakon ƙarancin fassara sadarwa tsakanin ma’aikatan agaji da al’umar Rohingya ya kasance – kuma ya na da matuƙar wahala. Mun tura wata tawaga zuwa Cox’s Bazar, Bangladesh, don gina ayyukan harshe da albarkatu don sauƙaƙe sadarwa da taimakawa inganta martanin jin ƙai.

A yau, akwai kusan ƴan Rohingya 900,000 a sansanonin ƴan gudun hijira a Bangladesh. Da har yanzu ke fuskantar wahala da neman taimako. Muna da ofisoshi na dindindin da ƙwararrun tawagar Bangladesh da ke aiki tuƙuru don taimakawa mutanen Rohingya samun bayanan da su ke buƙata da fahimta. Mun ƙirƙiri albarkatu da yawa  akan al’adun Rohingya, bayanai da buƙatun sadarwa da abubuwan da ake so , kuma mun kammala ayyuka 49. Kuma za mu ci gaba da yi.

Kamus na yaren Rohingya da takardun tantancewa 

Kamus ɗinmu na yaren Rohingya na Myanmar da Bangladesh na taimakawa sadarwa tsakanin ma’aikatan agaji da al’ummar Rohingya tare da fassara mai inganci da amfani kuma mai fa’ida. Takardun tantancewa ta harshen Rohingya cike take da fahimtar harshen.

Zaɓuɓɓukan bayanan Rohingya da ra’ayoyi

Ɗaya daga cikin rahotanninmu na baya-bayan nan na taimakawa fahimtar abubuwan da Rohingya ke so idan ya zo ga yaruka da tsarin da suke karɓar bayanai. Tare da sauran albarkatun buƙatun harshe, wannan binciken ya sauƙaƙe sadarwa da fahimtar al’adu.

Hanyoyin korafe-korafe da martani: mata da mutanen da ke da taƙaitacciyar zirga-zirga

A martanin ƴan gudun hijira, mu na taimakawa don tabbatar da sadarwa ta hanyoyi biyu, tare da cewa an ji muryoyin al’uma, ko su wane ne su. Mun yi hira da mazauna sansani a Rohingya game da faɗar ra’ayi da yin ƙorafi. Ana samun sakamakon bincikenmu da shawarwarinmu a cikin wannan rahoto.

Martanin ƴan gudun hijira na Turai

Mun ƙaddamar da shirinmu na amsar Fassarar Kalmomin Taimako a Satumban 2015. Manufar ita ce tallafawa ƙungiyoyin jin ƙai na cikin gida da na ƙasa da ƙasa waɗanda ke taimaka wa ƴan gudun hijira da baƙin haure da ke shigowa galibi daga Siriya, Afghanistan, da Pakistan. Mun fassara kusan ƙunshin kalmomi 800,000 zuwa Larabci, Farsi, Greek, Kurdish, da Urdu. Ƙungiyoyi abokan hulɗarmu sun ƙiyasta cewa mun taimaka wa kimanin mutane 100,000 don samun bayanai game da kariya, hanyoyin mafaka, da kuma ayyuka na yau da kullum a cikin harshensu.

Kuma mun shirya tarukan horarwa kai tsaye ga masu fassara, sannan mun ƙirƙiri ƙamus na harshe, takaddun gaskiya, da rahotannin tantancewar sadarwa don masu amsawa don ingantacciyar sadarwa tare da, saurare da magance bukatun ƴan gudun hijira. Ku na iya samun wasu abubuwan anan ƙasa.

European refugee response - Greece

Harshe da rashin fahimta a rikicin ayyukan jin ƙai na Girka – taƙaitaccen bayani

Wannan shi ne taƙaitaccen binciken da TWB da Save the Children su ka gudanar a Afrilun 2017 game shingen harshe da sadarwa dangane da matsalar ayyukan jin ƙai da ake fama da shi a ƙasar Girka.

Ayyukan yare na TWB game da martanin ƴan gudun hijira na Turai

Koyi game da ayyukan da mu ke yi ta shirinmu na Fassarar Ayyukan Taimako a zaman wani ɓangare na martanin ƴan gudun hijira na 2015 a Girka. Sannan kuma mu na bayar da tallafi kyauta ga abokan hulɗarmu da sauran masu amsawa.

Ƙamus na harshe da takaddun gaskiya

Takardun bayanan mu na Larabci, Kurdawa, , Farsi da Dari da  ƙamus na martanin ƴan gudun hijira na Girka na taimakawa masu amsa koyon wani abu game da ƴan gudun hijira ke magana, don inganta sadarwa da martanin ƴan gudun hijira.

Chatbot Planeta Azul OIM

Martanin ƴan gudun hijira na Latin Amurka

Tare da haɗin gwiwa da Ƙungiyar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Ƙasa da ƙasa ta Duniya, mun ƙirƙiri manhajar chatbot ta magana da Mutanen Espanya don ƴan gudun hijirar Venezuelan da ƴan gudun hijira a Peru da Ecuador, da kuma ƴan gudun hijira na Amurka ta tsakiya da masu neman mafaka a Mexico.

A matsayin shirin kwamfuta da ke kwaikwayon tattaunawar ɗan adam akan ƙa’idodi da na’urori, Planeta Azul OIM ta ba da mahimman bayanai game da ayyukan IOM, da sauran batutuwa masu ban sha’awa ga al’ummar da abin ya shafa. Wannan chatbot na amsa tambayoyin mutane a ainihin lokacin, kuma ya ƙirƙiri ƙwarewar tattaunawa ta hanyar rubutu da bidiyo. Ta wannan hanyar, mutane za su iya yin hulɗa da chatbot a cikin yaren su, kuma su karɓi bayanan da su ke buƙata da fahimta – ba tare da la’akari da matakin karatunsu ko kalmomin da aka yi amfani da su ba.

Mutanen da ke hijira daga ƙasashensu na asali na buƙatar kuma sun cancanci samun mahimman bayanai kuma a ji su, da kowane irin yare da suke magana, a duk inda su ka fito. Shi ya sa shirye-shiryenmu ke mayar da martani na ƴan gudun hijira ke ci gaba da bunƙasa. Tare da bayanan harshen mu, ayyuka, da fasaha, za mu iya isa da taimaka wa ƙarin mutane. Da fatan za a tallafa mana a aikinmu.