Game da tattaunawar biliyan huɗu
sauyin yanayi
A CLEAR Global, mu na taimakawa mutane a cikin yanayi na gaggawa su sami bayanan ceton rai, ko da wane yare su ke magana.
Matsalar ita ce: mutane na buƙatar bayanai don kare kansu daga bala’in sauyin yanayi
- Bala’an sauyin yanayi ya haura da kaso 83% cikin shekaru 50 da su ka gabata, wanda ya haifar da babbar ɓarna.
- Matsanancin yanayi na cutar da noma, tattalin arziki, da walwalar al’uma. Rukunin mutane ma su rauni, kamar mutanen da ke fama da rashin lafiya ko kuma ma su ƙarancin abubuwan rayuwa abin ya shafa.
- Rashin abinci ya ƙaru a cikin shekaru shida da su ka gabata, wanda ya shafi 30% na al’ummar duniya. Abubuwan amfanin gona na iya raguwa da kusan 30% nan da 2050, wanda zai dagula lamarin.
“Lokacin da guguwar Haiyan ta isa Philippines, Translators without Borders ta kai ɗauki cikin gaggawa, su na taimakawa wajen sanya idanu kan kafofin watsa labarun cikin yarurruka da fassarar rubutu da saƙonnin bidiyo. Tallafin ya taimaka wajen ceton rayuka da kuma bayar da tallafin isar da saƙo don sake hada iyalan da aka ceto."
Mafitar CLEAR Global
Ta hanyar samar da bayanan canjin yanayi a tsari da yaruka da yawa, CLEAR Global na taimakawa al’uma fahimtar sauyin yanayi da kuma matakan da za su iya ɗauka don shiryawa da kare kansu.
Ana amfani da bayananmu yare da kayan aikin sadarwa a cikin gaggawa don inganta sadarwa ta hanyoyi biyu tsakanin ma’aikatan jin ƙai da mutanen da bala’o’in sauyin yanayi ya shafa. Wannan na ba da damar martanin da ya fi dacewa ga rikicin, musamman a cikin al’uma daban-daban na yare waɗanda sau da yawa canjin yanayi ya fi shafa.
A Amurka, mun tura ƙungiyoyin mayar da martanin gaggawa a yanayin rikicin guguwa da yawa. Sama da mutane 100 sun yi aiki don fassara kalmomi 15,000 na jagora ma su muhimmanci kan sarrafa matsuguni, shirye-shirye don guguwa, da taimako zuwa yaruka shida.
A Nepal, ƙungiyarmu ta yi aiki 24/7 tare da hukumomin agaji masu taimakon farko don fassara saƙonni ga mutanen da girgizar ƙasa ta shafa, matsakaitan kafofin sada zumunta, fassara takaddun taimakon farko, da kuma rubuta bidiyo don inganta martani.
A Mozambique, bayan Cyclone Idai, mun ba da tallafin yare, gami da fassarar, bayanan yare, da taswira. Mun ba da bayanai masu muhimmanci a cikin yarurruka da yawa don taimaka wa mutane su koyi yadda za su kare kansu, samun mafaka, neman ƙarin tallafi, da sauransu.
CLEAR Global na buƙatar taimakonku don
martani ga sauyin yanayi.