Taswirar yaruka da bayanai

Ƙaddamar da bayanan yaruka na CLEAR Global na sanya yare akan taswira ta fannin jin kai da ci gaba.

Babu bayani mai yawa game da yarukan al’umar da rikici ya shafa wurin magana da fahimta. Ma’aikatan jin ƙai na haɓaka dabarun sadarwa ba tare da ingantattun bayanai game da ilimi ko yarukan da ake magana, ko hanyoyin sadarwar da aka fi so ba. Sakamakon hakan, sau tari mutanen da rikici ya shafa na fama da yadda za su yi magana da ma’aikatan agaji a yaren da su ke iya fahimta. Galibi mata, yara, dattijai, da masu buƙata ta musamman na cikin wahala sosai sakamakon ba su da tabbacin fahimtar harsunan ƙasa da ƙasa.

Muna tallafa wa ƙungiyoyi don haɓaka shirye-shirye masana ilimin harshe da dabarun sadarwa ta hanyar bincike da nazarin bayanan harshe.

Bayanai daga ƙasa

Ƙunshin bayanai da taswira don taimakawa fahimtar yarukan da ake magana da su a ina.

Tambayoyin yare

Tambayoyin da aka riga aka tsara da kuma fassara don tattara bayanan harshe.


Hangenku da ra’ayoyinku na iya taimaka mana mu sanya bayanan yare a matsayin mai isa da amfani sosai gwargwadon iko.

A tuntuɓe mu.

 

Ƙara koyo game da yanayin bayanan harshe a duniya, bincika taswirar labarin Bitar Bayanan Yarukan Duniya da dashboard..

Kayan aiki da albarkatu

Matakai guda biyar masu sauƙi don haɗa bayanan harshe cikin shirye-shiryen jin ƙai da haɓakawa

Bayanai kan harsunan mutanen da abin ya shafa na da mahimmanci don biyan buƙatunsu kamar yadda bayanai kan shekarun su da jinsi su ke. Wannan kayan aiki jagora ne mai sauri ga zaɓuɓɓukanku kan yadda ake amfani da bayanan yare a matakai daban-daban na tsarawa da isar da shirye-shiryen taimako.

Taƙaita: Nazarin buƙatun sassa da yawa na 2021 ya kamata ya tattara bayanai kan harsunan mutanen da abin ya shafa

Karanta taƙaitaccen bayani cikin Ingilishi koFaransanci.

Wannan taƙaitaccen bayani na bayar da hujjar cewa MSNAs wata muhimmiyar dama ce don ƙarfafa tushen shaida don ingantattun tsare-tsaren mayar da martani na ɗan adam. Ya na ba da shawarar yare da tambayoyin sadarwa, da muhimmin la’akari kan yadda za a haɗa su a cikin MSNAs.

 

Shafin yanar gizo: Bayanan yare sun cike babban giɓi ga ma’aikatan jin ƙai

Wannan shafin yanar gizon na ƙarin haske game da ƙoƙarin farko na samar da bayanan harshe a bayyane don yanayin ayyukan jin ƙai a ƙasashe tara. Ƙunshin bayanan sakamakon haɗin gwiwa ne tsakanin Translators without Borders da Kwalejin Jami’ar London.

Taswirar ilimi ta duniya ta jinsi

Wannan taswirar na nuna bambancin jinsi a cikin ilimin manya a kowace ƙasa. Ilimin mata ba shi da yawa idan aka kwatanta da na maza. Alama mai ruwan lemo na nuna ƙasashen da yawan ilimin maza ya fi na mata yawa. Alamar shuɗi na nuni da yadda ilimin mata ya fi na maza yawa a wasu ƙasashe da ba su da yawa.

Me ya sa mu ke buƙatar tattara bayanai kan yarukan mutanen da rikici ya shafa (PDF)

Wannan bayanin na nuna ƙalubalen da mu ke fuskanta lokacin da mu ka kasa haɗa bayanan yare cikin yanke shawara na ɗan adam. Domin magance waɗancan ƙalubalen, muna ba da shawarar tambayoyi guda huɗu waɗanda za su haɗa duk ƙoƙarin tattara bayanan ayyukan jin ƙai.

Duba bayanan bayanan cikin Ingilishi, Swahili na Kongo, Faransanci da Lingala (Facile) .

Bayanan yaren MSNA na iya taimakawa ma’aikatan jin ƙai sadarwa mafi kyau tare da mutanen da rikici ya shafa (PDF)

Wannan taƙaitaccen binciken yaren da sadarwa daga 2019 Multi- Sectoral Need Assessment a arewa maso gabashin Najeriya.. Ya kwatanta yiwuwar gudanar da manyan bincike irin wannan don cike muhimman harsuna da giɓin bayanan sadarwa a dukkanin jin ƙai.

 

Shafin yanar gizo: Lokacin da kalmomi suka gaza: naɗi sautin murya don tabbatarwa a cikin binciken yaruka da yawa

Wannan shafin yanar gizo na tattauna yiwuwar amfani da sautin murya don tabbatar da yarda da tabbatar da daidaiton sakamakon binciken da aka yi rikodin a cikin mahallin yaruka da yawa. Yana mayar da hankali kan aikin gwaji tsakanin Translators without Borders da Cibiyar Kula da Masu Gudun Hijirar Cikin Gida.

Jagorar ganowa da fassarar kayan aikin binciken cikin sauri

Wannan ɗan gajeren jagorar na taimaka wa hukumomin agaji da cigaba su gujewa son zuciya da harshe da al’adu lokacin tsarawa da gudanar da bincike. Wannan jagora Translators without Borders da Mutane ma su buƙata ne su ka samar da wannan jagora. Ana samunsa a shafin yanar gizon IndiKit da Ingilishi, Faransanci, da yaren Portigal.

Kalmomin da ke tsakaninmu: Ko masu ƙididdiga sun fahimci kalmomin da aka yi amfani da su a binciken jin ƙai?

Wannan rahoto ya nuna cewa yaruka ba abin la’akari ba ne na yau da kullun a yanayin binciken. Ya ƙare da cewa masu ƙididdiga sau da yawa ba sa fahimtar kalmomin da dole ne su fassara a cikin bincike.

Sanya harshe akan taswira a cikin martanin ƴan gudun hijira na Turai

Wannan rahoto ya nuna ƙalubalen da ke tattare da rashin samun ingantattun bayanai kan harshe a cikin rikice-rikicen jin ƙai. Yana mayar da hankali kan kimantawa da aka gudanar a Girka, Italiya, da Turkiyya tare da haɓaka jerin shawarwari waɗanda su ka ci gaba da zama tushen bayanan Harshen TWB.