Harkokin kuɗi

Gaskiya ita ce jagorar ayyukanmu a CLEAR Global. Mu na bin jagorancin ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke sa ido kan lissafin kuɗi, gami da GuideStar da Cibiyar Gidauniyar, waɗanda ke shawartar dukkan ƙungiyoyin sa-kai da su kiyaye gaskiya ta hanyar bayyana bayanan kuɗi, kamar Fom 990.

Ana samun takamaiman bayanai game da kuɗaɗen CLEAR Global akan Fom 990 ɗin mu, bayanin da ƙungiyoyin da ba su biyan haraji ke aikawa kowace shekara tare da Hukumar Harajin Cikin Gida Ta Ƙasar Amurka.

Da fatan za a lura cewa an yi wa Fom 990 laƙabi da ranar da aka fara, a kwanan watan shekarar kuɗi, amma ya ƙunshi bayanai har zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekara mai zuwa. Wannan lokacin daidai yake da shekarar kasafin kuɗin CLEAR Global, wanda a ka yi wa laƙabi da ranar ƙarshe ta shekarar kuɗi.

Hakazalika, an yi mana rijista a hukumance a matsayin Translators without Borders kafin shekarar 2021.