Translators without Borders (TWB) ƙungiya ce ta masana harsuna ta duniya waɗanda ke taimaka wa mutane samun muhimman bayanai kuma a ji su, ko da wane yare su ke magana.

Mutanen da ke magana da yarukan da ware galiɓi su na rasa muhimman bayanai a cikin yarensu. Ma’aikatanmu masana harsuna sama da 100,000 na bayar da gudummawar lokacinsu da ƙwarewarsu don fassara muhimman bayanai ga miliyoyin mutane a duniya, don haka kowa yana da bayanan da su ke buƙata kuma su ke so.

"Abu ne mai daɗi da sanyaya zuciya sosai kuma abin so a ga mutane na bayar da gudummawar lokacinsu da ƙwarewarsu don kare ƙa'idojin aiki da kuma ra'ayoyin taimakon jin ƙai."

Ƙarancin bayanan da aka fassara

Masu magana da yarukan da ware galibi ba sa iya samun damar bayanan da su ke buƙata kuma su ke so a cikin yare da tsarin da su ka fahimta. Wannan na hana su samun bayanai game da lafiya, koyo ko haƙƙoƙinsu.

Ƙungiyoyin sa-kai da sauran ƙungiyoyin duniya na iya rasa ƙwarewa ko kuɗi don sadarwa da mutanen da su ke
magana da waɗannan yaruka. Za su iya fuskantar matsalar nemo masu fassara a waɗannan yaruka ko ƙoƙarin dogara ga ma’aikatan gida don fassara, da hakan ke haifar da ƙarancin sahihanci bayanai, da ma’aikata da aka gajiyar da aiki.
Akwai buƙatar daidaita ƙungiyoyin jin kai da ƙungiyoyin sa-kai da ƙwararrun masu fassara a duk faɗin duniya. A nan ne Translators without Borders za su shigo.

Ƙungiyar masana harsuna ta duniya

Ma’aikatanmu na bayar da gudunmawar fassarar kalmomi sama da miliyan 20 duk shekara. Su na fassara bayanai ga ƙungiyoyi a duk faɗin duniya, su na aiki a cikin yarurruka sama da 200 — daga Amharic zuwa Zulu.

Mu na shirin ci gaba da haɓakawa da tallafawa ma’aikatanmu masana yaruka. Mu na samar da ma su fassara cikin yaruka ma su muhimmanci, mu na tallafawa sababbin ma su fassara haɓaka ƙwarewarsu da hanyar sadarwa. Mu na haɓaka fasahar yarurrukan mu, inganta dandalinmu da kuma haɗe sababbin fasahar harsuna don baiwa ma’aikatanmu kayan aikin da su ke buƙata don yin nasara. Kuma mu na ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu a duk faɗin duniya don haɗa ma su fassara da ƙwarewarsu da mutanen da ke buƙatar bayanai.

Za ku iya taimakawa

Za ku iya tallafawa ma’aikatanmu naTranslators without Borders ta hanyar gudummawa, tallafi ko ta amfani da ƙwarewar ku a matsayin masanin yare.
Zama ɗaya daga cikin ma’aikatanmu ta hanyar ziyartar shafin TWB.