Taimakon Harshe na Gaggawa ga Girgizar Ƙasa a Turkiyya-Syria
Tallafin fassarar kyauta – sadarwa tare da jama’ar da girgizar ƙasa ta shafa a Turkiyya da Siriya.
Miliyoyin jama’a ne girgizar ƙasa ta shafa, a yankunan Turkiyya da Siriya inda tuni miliyoyin al’uma su ka rasa matsugunansu. Jama’a na buƙatar matsuguni, sutura, abinci, da labarin inda za su iya samun tallafi. A wannan yanki mai yaruka daban-daban, yana da mahimmanci jama’a su sami labari kuma a ji su, da kowane harshe su ke magana.
Don samun buƙatun al’umma ma su kwararowa cikin sauri, CLEAR Global ta ƙaddamar da shirin Haɗin gwiwa na Fassarar Gaggawa na Al’umma.
Zan iya neman tallafin fassarar kyauta?
Ƙungiyoyin sa-kai da su ka cancanta waɗanda su ka haɗa da ƙungiyoyin gida, ƙungiyoyin al’umma, da ɗaiɗaikun mutane da ke tallafawa mutanen da girgizar ƙasa ta Türkiyya-Syria ta shafa na iya samun tallafin fassara kyauta.
Da waɗanne yaruka zan iya samun tallafin fassara?
Akwai tallafin fassara kyauta donTurkawa da kuma Larabci, karon farko.
Sauran yarukaa, gami da yarukan Kurdawa, akwai su – don Allah a tuntuɓe mu don tattaunawa.
Ta yaya Shirin Haɗin gwiwar Fassarar Gaggawa ke aiki?
Za ku sami tallafin fassarar kyauta don yarukan da su ka dace ta hanyar dandalinTWB na farkon watanni uku (da ake sabuntawa idan akwai buƙata).
Ma’aikatan mu naTWB za su fassara rubutattun takardu musamman masu alaka da rikicin, kamar:
- hijira cikin aminci, kariya, isa ga ayyuka
- takardun da ke fuskantar jama’a ko waɗanda aka ƙirƙira don ma’aikatan jin ƙai da sauran ma‘aikatan agaji,
- takardun da su ka dace da jagorancin UN, da
- takardun da su ka dace don kare masu amfani ta hanyar buɗaɗɗun takardun shiga da kyauta
Albarkatun harsuna da yawa don masu amsawa da mutanen da abin ya shafa
Taimakawa mutanen da girgizar ƙasar Turkiyya-Syria ta shafa su sami muhimman bayanai da tallafi Haɓaka sadarwa ta hanyoyi biyu da lissafi tare da albarkatu a cikin yarukan da suka dace:
- Dubi bayananmu nagaggawa kanbatutuwan harshe- Girgiza kasar Turkiyya-Syria
- ƙamus na PSEA, ciki har da yarukan Kurdawa guda uku da Larabci
- saƙonnin PSEA (daga IASC zaunannen kwamitin) cikin Larabci da TurKanci.
- Taskar Bayanan Harshen ƙurdawa
- “Babu uzuri ga cin zarafi” – horarwa kan PSEA a Kurdish Kurmanji, Turkiyya, daLarabci
- Ƙa’idodin PSEA masu bayyanannen harshe a cikin yaruka 100+.
- Kare albarkatu da Cibiyar Tallafawacikin Larabci.
- Dabarun harshe 20+ don ingantaccen tattara bayanan jin ƙai cikin Larabci
- Jagoran fassara don ma’aikatan jin ƙai na sansani a harshen Larabci
Jami’an agaji na ci gaba da tantance mutanen da suka rasa gidajensu. Taimaka don tabbatar da cewa za su iya samun taimako da bayani cikin yarensu.
Mutanen da abin ya shafa na magana aƙalla da harsuna huɗu, kuma mazaunan ƙasashen duniya na magana da yawa. Duk wɗannan mutanen na cikin haɗari.
Muna buƙatar tabbatar da aminci da bayanan kariya na samuwa a garesu baki ɗaya – da kowane yare da su ke magana, a duk inda su ke. Yawancin ƙungiyoyin gida na ƙasashe masu masaukin baƙi ba su da ƙarfin yarukan da ake buƙata don ingantaccen ayyukan jin ƙai.
Amma, za ku iya taimakawa a canza wannan.
Taimaka mana ƙirƙirar ƙarin ayyukan bayanan harshe, horarwa da tara mutane da yawa, da samar da ingantaccen tallafi ga sauran ƙungiyoyin da ke tallafin girgizar ƙasa.
"Mata ta ba ta jin yaren Turkish, sannan kuma ba na iya gani sosai."
– Wani mutum na ƙoƙarin gano ƴan uwansu da su ka ɓata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, Labaran BBC.
Taimaka da cire shingen harshe ga mutanen da rikicin ya shafa.
Ta yaya gudummawar ku ke taimakawa?
Gudunmawar ku za ta taimake mu:
- Yi la’akari da buƙatu kuma ku tabbatar da cewa ƙungiyoyin agaji sun sami damar yin amfani da ayyukanmu.
- Yi fassarar ayyukan al’uma ga ƙungiyoyin gida waɗanda su ne farkon masu amsawa ga mutanen da ke hijira,
- Goyi bayan masu bada ayyukan harshe na gida,
- Fassara mahimman takardun da ke taimakawa kare mutane ta hanyar hana cin zarafin jima’i da cin zarafi,
- Samar da kayan bayar da horo da shawarwari ga masu fassara a sansani, da kuma haɓakawa da bayar da horo ta yanar gizo.
Sami tallafin harshe don wasu ayyiuka
Ba da gudummmawa don tallafawa alklnmu
Gudunmawarku na taimaka mana wajen samar da ayyukan harshe da wuri don mu gina sabbin mafita ga jama’ar da yaƙi ya shafa.
Bayar da tallafin fassara
Yi aikin sa kai tare da mu.
Bayyana gwanintarka ta harshe ga aikin ƙwarai. Shiga TWB don taimakawa aikin gaji.