Harshe shine mabuɗin
Cimma Manufofin Ci Gaba Mai Ɗorewa:
Yadda ba za a bar kowa a baya ba–da kowane harshe da suke magana
Abubuwan da aka mayar na gida na taimakawa don samar da yanayin mataki mai kyau ga waɗanda abin yafi shafa.
Shigar da bayanan mafita kan lafiya, bincike da fasahar zamani zai taimaka wurin samun lafiya ga kowa.
Don taimaka wa al’uma samun mahimman bayanai, kuma a saurare su, da duk irin harshen da su ke magana.
Muna cim ma wannan manufa ta hanyar sabbin bincike da shirye-shirye na duniya, fasahar harshe, cibiyoyin harshe, ƙwararrun ma’aikata, da kuma al’umma sama da 100,000 a cikin ƙasashe 148 na masana harshe.
Ko dai ta manhajar COVID-19 chatbot a Najeriya, horar da masu fassara a Kenya ko binciken harshe a sansanonin ƴan gudun hijirar Rohingya, aikinmu na taimaka wa ƙungiyoyi don sadarwa yadda ya kamata, ta yadda za su iya isa ga mutane da yawa, su saurara yadda ya kamata cikin tasiri mai sauri.
28%
Kaso 28% na ƴan gudun hijirar Rohingya da aka yi nazari a 2018 waɗanda su ka ce ba su da isasshen bayanai don yanke shawara.
Biliyan 4
Akwai kusan mutane biliyan 4 da ke magana da harshen da aka ware, wanda a ke barin su a baya wurin tattaunawa mai muhimmanci a duniya.
80+i
Mun tallafa wa shirye-shirye da abokan hulɗa cikin ƙasashe sama da 80, a harsuna sama da 220.
Sababbin hanyoyin ƙarfafa gwiwar al’uma ta hanyar harshe da fasaha
Translators without Borders
Ƙarfin ikon ma’aikatan sa kai masana harsuna sama da 100,000 da ke sadaukar da kai don cike giɓin yarukan duniya da kuma ba da martani wurin amsa buƙatunsu cikin sauƙi.
CLEAR Tech
Mu na kan gaba wurin ƙwarewar fasaha don hulɗa da ƙarin jama'a ta hanyoyin da su ka fi dacewa da su.
CLEAR Insights
Mu na neman sababbin hanyoyin sauraron jama’a da gudanar da bincike don tabbatar da harshe da fasaha cikin aikin agaji.
Translators without Borders, mafi girman ma’aikata masana harsunan jin ƙai a duniya
Ma’aikatanmu masanan harsuna a duniya sama da100,000+ da ma su fassara ne ke tsakiya akan manufar mu. Ƙaunar su da ƙwarewar su na cike giɓin harshe a duniya baki ɗaya.
Dandalin TWB
Dandalin mu na sadar da NGO’s da ƙwararru a fannin harshe don samar da ayyukan lafiya da na jin ƙai, da bayanan haƙƙin ɗan adam a harsunan gida.
Ayyukan harsuna
Ayyukanmu na harsuna na taimakawa ƙungiyoyin sa-kai na duniya da na gida wurin hulɗa da mutanen da ke rayuwa cikin rikice-rikice. Mu na taimakawa wurin isar da muhimman bayanai cikin sauri, a harshen da ya dace.
Fasaha da magance matsalar bayanai
Ta hanyar horar da masu fassara da tafinta, da ƙirƙirar ƙamus na harsuna da yawa, da haɗin gwiwar bincike da fasaha., Mu na ƙarfafa bunƙasar harshe.
Ziyarci shafin intanet na Translators without Borders.
"Ban taɓa tsammanin za a iya ɗaukar harshe na da muhimmanci sosai har a saka a na'ura ba.”
Mai magana da yaren Waha, a Arewa Maso-Gabacin Nigeria
Sadarwa ta hanyoyi biyu na da mahimmanci. Fasaha na taimakawa wurin samun nasara. Gana da CLEAR Tech.
Mu na mayar da fasaharmu ta harshe zuwa abubuwa da ayyukan da su ka dace da yanayin gida, kuma waɗanda mutane da abokan hulɗa za su iya amfani da su cikin sauƙi.
Dabarun da za su yi nasara
Mu na amfani da fasahar sauti, manhajar AI, da fassarar na'ura wajen ƙara bunƙasa abu mai yawa da ingancin tattaunawar da ke kawo sauyi.
Dandalin da ke taimakawa
An gina fasahar mu ta zamo buɗaɗɗiya, don sauran masu ƙirƙira su iya shigar da ita cikin aikinsu. Hakan na ninka isarwa da kuma tasiri.
Ci gaba da isa, da saurare sosai
Mu na kan gaba wajen samar da sababbin hanyoyin cuɗanya da mutane a ko'ina - har ma a yankunan da ke da ƙarancin sadarwa da ƙarancin ilimi.
Koyi yadda za ku iya hulɗa da CLEAR Tech.
Sababbin hanyoyin saurare, kasance mai ɗaukar nauyi, da ƙarfafa ƙarfin tattaunawa. Gana da CLEAR Insights.
Harshe na iya hana samun tallafi. Shi ya sa mu ke fara saurare— sannan mu na gudanar da sababbin bincike don fahimtar abubuwan da mutane ke so na sadarwa da irin bayanan da su ke so kuma su ke buƙata. Mu na amfani da waɗannan bayanai don gano sabbin hanyoyin saurare— da kuma nuna wa duniya ƙarfin sadarwar haɗin kan al’umma.
Bayanan harshe da taswira
Taimakawa ma’aikatan agaji da sanin harshe da muhimmancin sadarwa na mutanen yanki, don su yi sadarwa mafi inganci da kuma shigar da ƙarin mutane.
Manazarta
Samar da nazarin harshe da kuma ‘tallafin farko da ake saurare’—wani muhimmin lamari na taimakon ƙasa-da-ƙasa.
Jagorori da bayanai
Yaɗa ayyuka mafiya kyawu aiki game da yaruka mafiya inganci, tsari, da hanyoyin ingantacciyar sadarwa.
Saurara CLEAR Insights ke farawa. Zamo wani ɓangare na mu.
Za ku iya taimakawa.
Wannan tsarin na aiki. Buƙatun na da yawa—ana barin mutane da yawa a baya kowace rana, saboda harshe da su ke magana da shi. An tabbatar da hakan – ba sau ɗaya ba. Amma mu na buƙatar kuɗi don haɓakawa.
Mun zarce yadda ake tsammani.
A da ana kiran CLEAR Global da Translators without Borders. Mun bunƙasa cikin gaggawa cikin shekaru biyar da su ka wuce, sai dai wancan sunan ba ya wakiltar dukkanin ayyukanmu—amma har yanzu ya na kasancewa wani babban jigo na ayyukanmu. Ziyarci shafin yanar gizon TWB anan.