CLEAR Insights logo

Mu na saurare, a CLEAR Insights.

Abin mamaki akwai bayani kaɗan a duniya game da harsunan da mutane ke magana da su, su ka fi so, da fahimta. Akwai
ƙarancin bayanai game da tushen bayanan da su ka amincewa da su. Hakan na sa wa ya zama da wahala ga masu aikin jin ƙai, ƙungiyoyin lafiya, da sauran masu sadarwa don sada bayanai cikin yare, hanya, da tsari mai dacewa.
Kuma yana ƙara zame masu da mai wahalar saurare. Da goyon bayan ku, za mu iya gudanar da bincike da tattara bayanai don sanar da dabarun sadarwa na duniya da na gida, da kuma tabbatar da an yi la’akari da buƙatun kowa.

“Mutanen da ke magana da yarukan da ake nuna wa wariya ba su da damar samun muhimman bayanai na ceton rai. Bugu da ƙari, galibin ƙungiyoyi ba za su iya aiwatar da su yadda ya kamata da kuma ba da martani ga mutanen da ke magana da waɗannan yaruka ba."

Giɓin bayanan yare

Domin akwai ƙarancin bayanai game da yarukan da mutane ke magana da fahimta, masu aikin jin ƙai da sauran masu sadarwa na duniya su kan ɗauka cewa yin amfani da yaren ƴan mulkin mallaka ya “ya isa”.

Duk da haka, a cikin bincikenmu a wurare, irin su Bangladesh, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, da Najeriya, mun ga cewa yin amfani da yare na kowa da kowa ba ya isa ga kowa. Sau da yawa ana barin mutane su ji kamar ba su da isasshen bayani don yin zaɓi da su ka dace da kansu da iyalansu.
Wannan hanyar ta sami matsaloli da dalilai na rauni. Mata, tsofaffi, masu buƙata ta musamman, da
mutanen da ke da ƙananan matakan ilimi ba sa iya magana da harsunan da ƙungiyoyin duniya ke amfani da su.
Su na da ƙarancin bayanai, da kuma ƙarancin hanyoyin shigar da damuwarsu da kuma fifiko. Su na ƙara dogaro ga wasu a cikin al’ummarsu don sadarwa.
Rashin wayar da kai game da buƙatar yin la’akari da yare a sadarwar duniya akai-akai ya kan haifar ƙarancin harshe kuɗin aiki da albarkatu ga fasahar sadarwa.
Wannan ya bar miliyoyin mutane ba tare da bayanan da suke buƙata ba, kuma ya na ci gaba da tsarin rashin saurare da la’akari da buƙatun mutanen da ke magana da yaruka masu ƙaramin ƙarfi. 
Mu na shirin canza wannan, kuma muna buƙatar taimakon ku.

Mafita na fahimtar yare

Mu mu na da tarihin bincike mai amfani da hanyoyin bayar da shawarwari da ke sanar da shirye-shirye da ayyuka masu la’akari da yare. Mun yi bincike kan mutanen Rohingya da ke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira a Bangladesh, mun yi nazarin yadda za a iya samar da hanyoyin sadarwa na sauti na yaruka da yawa a Najeriya, kuma mun ba da shawarar sauye-sauyen manyan matakai.

Yanzu, mu na da shiri don cike giɓin bayanan yare da giɓin bincike ta:
  • gudanar da ingantaccen bincike don ƙarin fahimtar buƙatun sadarwar mutane da ƙalubale,
  • tsara taswirar yarukan duniya don inganta sadarwar duniya, 
  • gina sabbin hanyoyin bincike da martani, waɗanda fasahar harshe ke ƙarfafawa, don sauraron mutanen da ke magana da yaruka masu ƙananan albarkatu, da
  • haɗin-gwiwa da ƙungiyoyin jin kai, haɓakawa, da ƙungiyoyin bincike don sanya yare da buƙatun sadarwa a ajandar ƙasa-da-ƙasa.

Za ku iya taimakawa.

Buƙatar bayanan yare, bincike da bayar da shawarwari don tabbatar da cewa an saurari masu magana da yarukan da ake nunawa
wariya. Taimakon ku na iya yin tasiri mai girma, isa ga mutane da yawa, a wurare da yawa, tare da ƙarin yarurruka.
Kasance cikin mafitar sadarwa ta duniya. Tuntuɓe mu, kuma za mu tuntube ku ba da jimawa ba.