Kira ga masu ɗaukar nauyi
Ɗauki nauyin CLEAR Global a yau
Damar ku ta kasance tare da mu a sahun gaba na bincike da fasahar yare na manhajar AI don amfanin zamantakewa.
Ku na da burin taimaka mana mu daidaita yaɗa dijital language?
Samar da tasirin zamantakewar gaskiya tare da mu.
CLEAR Global ta ƙaddamar da wani babban shiri don shawo kan ƙalubalen da ke hana ci gaban duniya. Mu na neman masu goyon bayan dabarun da ke yaɗahangen nesa don daidaito,da kuma son yin tasiri mai kyau a duk duniya.
Ku na amfani da ƙunshin fasaha, sadarwa, ko fannin fassara?
Shin kamfanin ku ya yi daidai da hangen mu, kuma a shirye yake ya yi aiki?
Mu na gayyatar ku don goya mana bayan tafiyar mu – ta Four Billion Conversations.
saboda har yanzu mutane biliyan huɗu ba sa iya samun bayanai ko sadarwa ta intanet cikin yarensu.
Idan kamfaninku ya sanya hannun jari don haɓaka tattaunawar yaruka da yawa, haɗin gwiwa, haɓakawa da ɗorewa, zama wani ɓangare na mu don amfanar kafar intanet ga kowa da kowa, a yarensa.
Bisa tallafin masu ɗaukar nauyinmu cikin girmamawa, CLEAR Global ta shirya kawo sauyi ga duniya ta fannin sadarwa. Ƙwararrun ma’aikatanmu na haɗin gwiwa na duniya tare da masu magana da yare na gida da masana fasaha don gina sabbin hanyoyin magance matsalar yare, gami da samun dama.
Mun riga mun samar da manhajar chatbot na tattaunawa a yaruka da yawa, ƙamus da sauran abubuwa na yanar gizo don taimakawa mutane su sami mahimman bayanai a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, da arewa maso gabashin Najeriya, Ukraine , Turkiyyya da Siriya, da sauransu.
Ma su ɗaukar nauyi da za su iya ba da gudummawar $25,000 ko fiye za su iya taimaka mana mu faɗaɗa ayyukanmu da haɓaka fasahar mu don isa ga al'umma da yawa a duniya.
Koyi yadda ɗaukar nauyinku zai iya taimakawa canza tsarin iko a duniya kuma ya haɗa da ƙarin mutane cikin muhimmiyar tattaunawa ta duniya, game da tilasta yin gudun hijira, lafiyar jama'a,kula da lafiyar mata masu juna biyu da haihuwa da haƙƙoƙinsu , da kuma sauyin yanayi.
Me ya sa za ka zamo mai ɗaukar nauyin CLEAR Global?
Zama ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyinmu, za ku taimaka mana wajen daidaita shirye-shiryen tallafin sadarwar mu da hanyoyin fasahar yare, don haka miliyoyin mutanen da ke magana da yarukan da ba a sani ba za su iya jin muryoyinsu kuma su sami mahimman bayanai da dama masu canza rayuwa. Za ku zamo wasu muhimman ɓangaren ƙungiyarmu.
A matsayinku na masu ɗaukar nauyi, kamfanin ku zai amfana ya sami ƙaruwa kuma a sanshi ya bunƙasa da samun haɗin gwiwa, da manyan ƙungiyoyin sa kai masu bayar da shawarwari ba don samun riba ba don ku sami shiga da rarrabewa . Duk masu ɗaukar nauyi za su ci gajiyar waɗannan fa’idodi masu zuwa:
- sanin irin kayan da su ke samarwa da kuma yabawa, a fannin yare ayyukan jin ƙai da makamantansu
- zuba jari mai manufa a matsayin wani ɓangare na dabarun haɗin gwiwar ku,
- tasiri kai tsaye – inganta rayuwar miliyoyin mutanen da ke magana da yarukan da aka ware,
- damar sanya kawunan ku a matsayin ƙwararru tare da bayar da gudummawa ga ƙirƙirar fasahar ci gaban harshe
- fahimtar harshe da bayanan sadarwa waɗanda za su iya taimaka mu ku daidaita hanyoyin magance matsalarku, da kuma isa ga mutane da yawa,
- masu sa kai na gida, horarwa da damar cigaban ma’aikatan ku,
- ƙarin shahara a kafafen sadarwa (shafin yanar gizo, imel, kafofin yaɗa labarai), da
- tasirin duniya ta hanyar tallafawa shiga cikin shirye-shiryen da ke taimakawa canza yanayin sadarwa mafi kyau
Wa ya kamata ya zama mai ɗaukar nauyin CLEAR Global?
Idan kamfanin ku na son:
- mayar da kafar intanet bigiren amfanin kowa da kowa, da duk irin yaren da su ke magana,
- inganta sadarwar yaruka da yawa don haɗin gwiwar duniya da ci gaba,
- tallafawa ci gaban harshe ta manhajar AI don haɓaka damar mutane ga samun bayanai, da kuma
- kiyaye ayyukan ƙungiyoyin duniya, abokan hulɗa na gida, da membobin al’umma
Tuntuɓemu don ganin yadda za mu yi aiki tare, da gina duniyar da ta haɗe yaruka.
Tallafawa aikin CLEAR Global tare da ayyukan ku na ci gaban al’uma
Haka kuma zaɓinmu na tallafin kuɗi , sannan kuma mu na maraba da ku don shiga ɗaukar nauyin duk wani shiri namu.
Idan ku na sha’awar ɗaukar nauyin aikinmu tare da ayyukan ci gaban al’uma, za ku iya la’akari da samar da:
- Tallafin fassara: haɗa gwiwa da mu don yin fassara, bita da gyaran ayyuka da ya danganta da abinda ku ka iya da nau’ikan yaren da ku ka fi so.
- Tallafi game da abinda ya shafi rikici:taimaka mana don biyan buƙatun alʻumar da abin ya shafa cikin gaggawa da haɓaka ayyukan jin ƙai cikin gaggawa ciki har da bala’o’i, rikicin siyasa ko zamantakewa, lafiyar jama’a da sauransu.)
- Taimakon fasaha :taimaka don faɗaɗa ayyukanmu da haɓaka mafita na manhajar AI da yaren tushen fasaha da shirye-shiryen bincike.
- Taimako na bayanai da fahimta: taimaka mana don bincikowa da haɓaka bayananmu ta yadda za mu iya ingantawa da haɓaka isar da saƙo
Gudunmawar ku a matsayin ma su ba da tallafi ta wannan nau’i na haɓaka tasirin da mu ke ƙirƙira a CLEAR Global tare da tallafin ma’ikatanmu na Translators without Borders.
Shirye-shiryen mu a wannan nau’in ya gano karimcin waɗanda ke bayar da lokacinsu, fasaha da ƙwarewar su don taimaka mana cimma burinmu. Masu irin wannan ɗaukar nauyi kuma na amfana ta hanyar shahara a mafi girman al’ummar duniya na masu aikin jin ƙai na sa kai da ci gaban harshe. Ƙara koyo game da TWB – ma’aikatanmu mu na duniya fiye da mutane 100,000.
Ma su ɗaukar nauyin mu
Ma su ɗaukar nauyinmu sun haɗa da kamfanoni da ƙungiyoyi daga masana’antu da yawa. Dukkansu sun taru don ba da gudummawa ga aikinmu na gama-gari, don taimakawa mutane su sami mahimman bayanai kuma a ji su da duk yaren da su ke magana. Mu na godiya ga:
Sannan mu na ƙara godiya da goyon bayan ma su tallafawa ma’aikatanmu na TWB. Ƙara sani game da su akanshafin TWB.
Kuma ta yaya kamfani na zai iya taimakawa?
Idan ku na neman taimakawa aikinmu, za ku iya ba da gudummawa mai girma. Gudunmawar ku za ta taimaka wajen samar da takamaiman ayyuka, waɗanda za mu iya yin la’akari da su tare. Irin wannan tallafin na da mahimmanci kuma ana yabawa – ayyuka yawanci su na buƙatar kuɗi tsakanin $25,000 da $100,000.