Ku na goyon bayan mutanen da yaƙin Ukraine ya shafa?
Waɗannan kayayyakin na ku ne.
Bayananmu da abubuwan da ake buƙata a aikace na iya taimaka mu ku wajen fuskantar ƙalubalen yare da sadarwa
– Aукраїнська, polski, Română, русский, Magyar, slovenčina, čeština, Deutsch.
Me ku ke son yi?
Latsa nan don tsallakawa zuwa sashen.
Yi sadarwa yadda ya kamata tsakanin harsuna
Yadda za a sami, aiki tare da, ko aiki a matsayin mai tafinta ko mai fassara a aikin jin ƙai na gaggawa.
Duba wannanƙunshin bayanan masu tafintadon tallafawa yaren da ke kusa da ku.
Sanar da muhimman batutuwan jin ƙai
A san irin kalmomin da za a yi amfani da su wurin sanar da kariya, ɗaukar nauyi da kare cin zarafi ta hanyar jima’i, keta haddi da matsantawa (PSEA) a aikin agaji a Ukraine. Samu damar maganganun masana da kayayyakin horarwa na harsunan da suka dace.
Jerin ma’ana a harsuna da yawa na PSEA – cikin Ingilishi– українська – polski –Română – русский – Magyar – slovenčina, čeština – Deutsch
Jerin ma’anonin kariya da ɗaukar nauyi na Oxfam – a Ingilishi – українська – polski – Română – русский
Ainihin ƙai’idoji da suka danganci cin zarafi da amfani da dama ta hanyar jima’i a harshe-mai sauƙi – a Ingilishi – українська – polski – Română, русский – Magyar – Deutsch
‘Ba Uzuri ga Cin Zarafi’ gabatarwar bidiyon PSEA ga sababbin masu aikin agaji da ƴan kwangila – A Ingilishi – українська – polski – Română – русский– Magyar – slovenčina – čeština – Deutsch
Dandalin Bayanan Amfani da Harshe kan Agaji a Ukraine
Dandalin musayar bayanai da ya hadar da kafofi masu yawa don bawa masu aikin agaji cikakkar dama da kuma sabuwar mahanga ta harsuna da kuma hanyoyin sadarwa da jama’ar da yaƙin Ukraine ya shafa ke amfani da su.
Taswirar yaren da ake hulɗa da shi don Ukraine
Bayanin da za a iya kalla wanda ke nuna wuraren da mutane ke magana da yaruka sama da ashirin da aka ɗauka a faɗin Ukraine.
Masu aikin agaji za su iya amfani da shi don fahimta sosai da tallafawa jama’ar da rikici ya shafa.
Yi amfani da kayan aikinmu ku tattaro bayananku game da buƙatun harshe da hulɗoɗiin mutanen da su ke amfani da ayyukan da ku ke yi.
An tanadi tambayoyi ga ɗaiɗaikun mutane, iyalai da jin ra’ayin muhimman masu ba da bayanai da aka tsara na Kobo Toolbox/ODK. An tanada a harshen čeština, Magyar, Română, русский, slovenčina, українська, Deutsch, polski, da Ingilishi a shafin yanar gizon TWB.
Miliyoyin jama’a sun yi hijira daga Ukraine. Sama da wasu Miliyoyin na neman mafaka a ƙasashen waje. Taimaka don tabbatar da sun samu muhimman bayanai cikin yarensu.
Yaɗa bayanai tare da jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine
Kompas wani dandalin harsuna ne masu yawa na na’ura mai fikirar dan Adam da ke ajiye bayanan da aka tantance, yanzu-yanzu don jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine a harsunan Ukrainian, Polish, Romanian da Russian. Wannan na taimakawa mutane samun amsoshin da su ka shafe su don su fahimci haƙƙoƙinsu, su sami taimako, kuma su yanke hukunci kan me za su yi nan gaba. Don tallafawa jama’a samun bayanai cikin sauƙi sosai a yaren da su ka fahimta, ƙungiyoyin bayar da agaji za su iya:
- Yaɗa bayananku ga jama’ar da yaƙin ya shafa ta hanyar Kompas
- Saka Kompas a shafin yanar gizonku don tallafawa mai amfani da ita sosai
- Tattauna ta yin amfani da Kompas a matsayin kayan aikin tawagar shirinku da masu ɗaukar layin waya
Don ƙara koyo, tuntuɓe mu.
Fahimci ƙalubalen sadarwa da jama’ar da su ke gujewa yaƙin Ukraine ke fuskanta a kasarku
Duba taswirar labaranmu don ganin muhimmancin yare ga mutanen da yaƙin Ukraine ya shafa, da dalilin hakan ga ingantaccen aikin agaji a Ukraine da ƙasashe maƙwabta
Karanta shaidar shigar da yaree cikin aiki agaji
Sadarwa ƙalubale ne cikin aikin agaji, ko da a wuraren masu amfani da ayyuka da masu samar da ayyukan ke magana da yare guda.
Mu na magana da mutanen da yaƙin ya shafa kai tsaye, ƙungiyoyin agaji, da masana harshe a ƙasashe uku da ke ɗaukar nauyin mafi yawan jama’ar da aka tilastawa tserewa daga Ukraine. Karanta hangenmu da shawarwarinmu na yadda ma’aikatan agaji za su magance tarnaƙi na harsuna kuma su harhaɗa tallafi ga yare don samun nasara kan manyan ƙalubale.
Amfani da yare da kuma asalin harshe na iya zama na takatsantsan, ana buƙatar ma’aikatan agaji su fahimci wadanne yaruka jama’a ke buƙata ko su ka zaɓi su yi hulda da su.
Karanta rahotonmu kan yadda amfani da yare da asalin harshe ke canzawa a Ukraine don fahimtarwaɗannan muhimman abubuwan sosai da tsara dabarun sadarwa da su ka dace kuma masu tasiri.
Kasance cikin samun sabon bayani
Shiga jerin waɗanda za mu aikawa saƙoza mu tura maka bayanan sabbin ayyukanmu.
Taimaka ya isa ga jama’a da yawa
Samu gudunmawar harshe
Ba da gudunmwa don tallafawa aikinmu
Gudunmawarku na taimaka mana wajen samar da ayyukan harshe da wuri don mu gina sabbin mafita ga jama’ar da yaƙi ya shafa.
Bayar da gudunmawar fassara
Yi aikin sa kai tare da mu.
Bayyana gwanintarka ta harshe ga aikin ƙwarai. Shiga TWB don taimakawa aikin gaji.