Game da tattaunawar biliyan huɗu

Lafiyar haihuwa da haƙƙoƙin mata

A CLEAR Global, mu na bai wa matasa mata da ƴan mata wuri mai aminci da sirri don yin tambayoyi, bayyana damuwa, da samun taimako, ko da wane yare su ke magana.

Matsalar ita ce: mata na buƙatar koyo da yin magana a fili game da lafiyarsu

  • Mata a duniya su na fuskantar ƙyama, da ke hana su fitowa fili da kuma samun bayanai game da lafiyar haifuwa da haƙƙoƙinsu.
  • Rashin samun bayanai da ilimi na jazawa mata, musamman ƴan mata da mata masu ƙananan shekaru, ga kamuwa da cututtuka daban-daban na jima’i (STIs). STIs na shafar lafiyar mata ta nuna mu su ƙyama, rashin haihuwa, har ma da ciwon daji da matsalolin juna biyu.
  • Sama da kaso 95% na mace-macen mata masu juna biyu na faruwa a ƙasashe ma su tasowa, sakamakon ƙarancin bayanan kiwon lafiya da ingantattun ayyuka su ne musabbabin.

"Kyakkyawar sadarwa na da mahimmanci idan za mu tabbatar da cewa mutanen da ake ƙyama waɗanda su ka sha wahala sosai za su sami tallafin da ya dace. Kashi uku na matan Rohingya da ke sansanonin sun ce ba su ji daɗin barin matsugunan su ba - mu na buƙatar cikakkiyar fahimtar abinda ya sa hakan ya kasance, don haka za mu iya yin kyakkyawan aiki na kare mata."

Dorothy Sang
Kamfen manaja na Oxfam a Cox’s Bazar

Mafitar CLEAR Global

CLEAR Global na haɗin-gwiwa da ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin mata da kiwon lafiyar mata don samun bayanan lafiyar jima’i da haihuwa a samar da su cikin yaruka da tsarin da mata ke fahimta. Da sabbin hanyoyin sadarwar mu, mata na iya samun albarkatun ilimi, ayyukan kiwon lafiya da tallafi. Haka kuma za su iya faɗar damuwarsu kuma su sami amsoshi cikin aminci da tsari.

Lokacin ayyukan ƙwayar cuta ta Zika, mun yi aiki tare da Hukumar Lafiya ta Duniya don samar da muhimman bidiyo tare da shawara ga mata ma su juna biyu da aka yi wa laƙabi da murya a yaren Creole na Haiti da yaren Fotugal na Brazil a Haiti da Brazil.

A Kenya, fassarar mu na kayan ilimi da fostocin kula da lafiya na asibitocin al’umma sun baiwa ma’aikatan kiwon lafiya na karkara da malamai damar isar da bayanai game da shawarwarin shayarwar jarirai a cikin harsuna na gida a karon farko.

Mun jagoranci ƙungiyoyin mayar da hankali don fahimtar yadda matan Rohingya a Bangladesh ke magana game da lafiyarsu da matsalolin su. Mun ƙirƙiri abubuwan harshe, kamar sautika da ƙamus, ga ma’aikatan agaji don magance buƙatun mata.

CLEAR Global na buƙatar taimakonku don

bai wa ƙarin mata hanyoyin koyo game da lafiyar haihuwa da haƙƙoƙinsu.