CLEAR Global na samarwa da abokan hulɗa aikin fassara ta cikin harsuna masu yawa ta amfani da Ma’aikatan TWB ta hanyar sadarwa daban-daban da kuma ma’aikatan sa kai sama da 100,000. Manufarsu guda ɗaya ce dukkansu ta haɓaka damar samun ilimi ta hanyar harshe da kuma tabbatar da an saurari waɗanda suka fi rauni a duniya.
Ƙarfin ƙwarewar Harshe na Ma’aikatan TWB
Wannan jerin Ƙwarewar harshe na Ma’aikatan TWB na taimakawa abokan hulɗarmu fahimtar abubuwan da muke da su don ayyuka a mabanbantan harsuna.
Bincika ginshiƙin Ƙarfin Harshen Ma’aikatan TWB – gano yanayin sauyin lokutan da suke ɗauka don ayyuka cikin harsuna daban-daban, dangane da ƙarfin ma’aikatanmu.
Dukanin ma’aikatan TWB na amfani da ra’ayoyinmu da ɗabi’u masu kyau tare da aminta da Ƙa’idojinmu na fassara.
CLEAR Global na bin matakan tabbatar da ingancin fassara don tabbatar da rukunin masu fassara na aikin kan kowane aiki, gami da ƙwararren mai bita dake bibiyar kowane aikin sauran ma’aikata.
Yanayin sauyin lokacin gudanar da ayyukan Harshe
Yayin da abokan hulɗar CLEAR Global ka iya buƙatar aikin fassara a duk harsuna biyu, muna da jagorar da ya kamata ku sani. Wannan samfur mai zuwa a ƙasa shine jerin harsunan da ma’aikatan sa kai ke da ikon yi.
idan harshe na cikin jeri ƙarshin Daidaitaccen lokacin da ya dace(TATs), na nufin muna aiki akai-akai a wannan harshe kuma gabaɗaya muna iya isar da fassarar da bita ba tare da ƙarin kuɗi ba, daidai da Jagororin Ayyuka da muke Amfani da su. .
Haka kuma CLEAR Global na yin fassarar wasu harsuna da ke da ƙarancin masu fassarar sa kai da hakan ke kawo. tsawaitar lokaci. Don haka muna roƙon da a bamu lokaci yayin da aka buƙaci fassara a wannan harsuna. Idan CLEAR Global ta gaza samar da mai fassarar wannan harshe, za mu sanar da ku akan lokaci.
Ƙarin harsuna ƙarin ayyukan fassarar harshe
Tuntuɓe mu don tattauna dabarun fassara harshenku
- idan kuna neman wasu harsunan da banbanta na gida da babu su a wannan jeri,
- domin tattauna ayyukan harshe ba ta fassara ko bita ba (ɗora murya, fassarar murya buga rubutu, gyara harshe zuwa sassauƙa, mayar da manhaja/shafin yanar gizo zuwa harshen gida, mayar da sauti zuwa rubutu, buga takardu, ƙamus da tattara bayanai, tabbatarwa da sauransu.)
Bunƙasa ƙarfin harshe
CLEAR Global za ta yi ƙoƙarin isar da ayyuka a kowane harsuna biyu don biyan buƙatun ƙungiyoyin abokan hulɗarmu, idan an bayar da abinda aka buƙata.
Yayinda da muke aiki da harsunan da muke buƙatar gano abubuwan dogaro da haɓaka al’umma mai ƙarfi, CLEAR Global ta samar da hanyar bayar da horo. Wannan na ƙarfafa sabbin ma’aikatan harshe na sa kai haɓaka ƙwarewarsu tare da mu, da kuma ba abokan hulɗa damar cin gajiyar ƙwarewar harshen su yayin da suke samun ƙwarewa don aiki na gaba.
Mu kan yi aiki da ƙungyoyin abokan hulɗa, lokaci zuwa lokaci don ɗaukar ma’aikatan sa kai a Ma’aikatan TWB don warewa harsuna masu ƙarancin tsarin gina fasaharsu.