
CLEAR Tech zai kawo sauyi ta fannin sadarwa ga mabanbantan.
Rashin samun daidaiton sadarwa da samun damar bayanai. Ba a samun bayanai cikin yarukan da aka ware.
Waɗannan su ne yarukan al’umar da ba su da ƙarfin iko, kuɗi ko tasiri a duniya. A hannu guda kuma, mutanen da suka fi buƙatar bayanai ba za su iya samun su ba. Muna gina sabbin fasahihohin harshe don ingantawa bisa goyon bayanku, don haka kowa na da abin cewa.

"Sadarwa ita ce ainihin abinda ake buƙata da zai iya taimakawa don ceto da kare rayuka."
Editor, TC World
Matsalar giɓin yare
Mu na tattaunawa game da rarrabuwar fasaha. Amma yanzu muna ganin rarrabuwar yare – da kuma giɓi tsakanin mutanen da ke magana da yaruka masu ƙarfin kasuwanci da kuma duniya da waɗanda ke magana da yarurrukan da ba su da ƙarfi. Wannan giɓin na ƙaruwa a kowace rana.
Mutanen da ke magana da yaruka masu ƙarfi ba kasafai su ke shan wahalar samun bayanai cikin yarensu ba. Kuma ingantacciyar fasahar yare na ba da damar sababbin bayanan da za a fassara akai-akai cikin inganci.
Amma ga al’umar da ba za magana da yare mai ƙarfi, ba su cika samun bayanai yadda ya kamata ba. Babu fasahar yare don ƙirƙirar sabbin bayanai. Wannan bambance-bambancen na haifar da giɓin bayanai da ke ƙara faɗaɗa nan da nan.
Akwai buƙatar gaggawa, don haka mu na buƙatar taimakonku.



