Game da tattaunawar biliyan huɗu

gudun hijira da aka tilasta

A CLEAR Global, na taimaka wa ƴan gudun hijira da baƙin haure su sami muhimman bayanai kuma a ji su, ko da da wane yare su ke magana.

Matsalar ita ce: shingayen yare na shafar haɗin kan zamantakewar al’umma

  • Ya zuwa shekarar 2022, an tilasta wa sama da mutane miliyan 100 barin ƙasashensu saboda tashe-tashen hankula, ƙarancin abinci, matsalar yanayi ko wasu matsalolin gaggawa.
  • Shingayen yare na sa wa ƴan gudun hijira da baƙin haure wahalar samun aiki, ilimi, tallafi mai muhimmanci da ayyuka, kamar kiwon lafiya da gidaje.
  • Ƙasashe masu masaukin baƙi da ƙungiyoyin agaji sau da yawa ba sa jin yare da don ƙarin fahimta da taimaka wa mutanen da ke neman mafaka.

"Mun yi wasu abubuwan mamaki a nan... samar hanyoyin da su ka kasance a cikin tsarin da ke samuwa ga kowa."

Refucomm
Haɗin gwiwa da Girka/Words of Relief

Mafitar CLEAR Global

CLEAR Global na yin bincike akan yarukan mutane, buƙatun bayanai, da abubuwan da ake so. Hangenmu na taimakawa ƙirƙirar hanyoyin sadarwar da mutane ke jin daɗin amfani da su don samun bayanan da su ka amince da su kuma su ka fahimta. Ta wannan hanyar, mutanen da aka tilasta wa yin hijira za su iya samun ayyukan ceton rai wanda su ka dace da buƙatunsu da yanayinsu.

A ƙasar Girka, ta hanyar shirin mu na Words of Relief, mun yi aiki tare da kungiyoyi 20+, kuma mun horar da ma’aikata 200+ da masu sa kai kan sadarwar al’adu. Mun fassara kalmomi 800,000+ zuwa aƙalla yaruka takwas don biyan buƙatun ƴan gudun hijirar da yawa.

A Bangladesh da Myanmar, mu na aiki tare da ƙungiyoyi masu tallafa wa mutanen Rohingya tun 2017. Mu na ci gaba da bayar da tallafin yare da bincike don sanar da martanin jin ƙai da inganta sadarwa mafi kyau ta hanyoyi biyu.

A Ukraine, mun hanzarta tattara kayanmu mu don taimakawa mutanen da aka tilastawa barin ƙasar. Mun yi aiki tare da ƙungiyoyin gida da na waje guda 49, a ayyukan gaggawa 276 waɗanda su ka haifar da fassara kalmomi miliyan 1.5 zuwa yaruka 35.

A Latin Amurka, mun yi haɗin gwiwa da Kula da Masu Gudun Hijira ta Duniya a Ecuador, Mexico, da Peru don ƙirƙirar manhajar Planeta Azul, mataimakiya ga chatbot. Manhajar chatbot ɗin ya taimaka wa mutane samun dama ga muhimman ayyuka da bayanai a iyakar Amurka da Mexico.

CLEAR Global na buƙatar taimakonku don samarwa da ƙarin ƴan gudun hijira da baƙi bayanan ceton rai.